Jam’iyyar APC tace PDP baza ta iya bada wani kyakyawan adawa ba Idan Jami’in su mai hudda da Jama’a ya ci gaba da maganganun marasa tushe.
Idan za’a iya tunawa, a ranar 26 ga watan Yuli, Jam’iyyar PDP ta lissafa wasu abubuwa data kira “Zunubban Buhari”, idan har ta zargi shugaban da zubadda mutuncin Najeriya a Amurka.
Jaridar Vanguard a rahotannin tace, APC ta maida martani inda kakkakin, Lai Muhammad ya maida martani a ranar. Yace: “A yau ma dai Jam’iyyar PDP ta fidda wani tsokaci Wanda yafi kama da surutan mashayar giya, ba wai tsokaci akan gwamnati mai ci ba. Zama Jam’iyyar adawa ba wai zuwa gidagen jaridu bane da duk wani labari daya tari gaban ka. Ingancin maganganu ne ke sanya Jam’iyyar adawa tayi mutunci, ba wai yawan tsegumi marar tushe ba a Damakuradiyyance. APC ba zata maida martani aka wannan zancen marar tushe ba na Jam’iyyar adwan ba.
“Lallai munyi gaskiya da kuma kokarin kwatantama mutane cewa Metuh na bukatar fadakarwa akan yadda zaya gudanar da aikin shi. A lokacin da Muka yi mashi tayin yazo mu koya mashi, wasu sun dauka wasa mukeyi. Amma yanzu kowa ya gani. Yana bukatar jagoranci akan yadda zaya gudanar da sabon aikin nashi. Shugaba Buhari ya maida hankalin shi ne akan yadda zaya dawo da shugabanci na gari, musamman yadda Jam’iyya marar kunya, marar hankali, PDP tayi ba.”
Sannan kuma yace: ”Shugaban Amurka Obama ya yaba Buhari da cewa shi Buhari mai aminci ne, mai kudurori masu kyau. Buhari yana kokari na musamman bangaren wajaje masu muhimmanci, tsaro, rashawa, da kuma yadda zaya habbaka tattalin arziki domin matasanmu su samu aikinyi. Muna tausayama wadanda suka makamce basu gane hakan ba.”
“Munsan Jam’iyyar PDP ta fusata akan yadda gwamnatin tarayya data jagoranta tayi almundahan, ta kuma bada yanayin da zalunci yayi karfi, sannan kuma tana sane da abunda zaya faru da wadanda suka aikata aiyyukan rashin kyautawar ba da zubadda mutunci. “Gwamnatin Buhari ba zata ringa sanya hannu cikin aikin Jami’an tsaro ba, da kuma aikin Jami’an Hukumar hana almundahana (EFCC). Wadanda kawai za suji tsoro sai dai masu laifi. Babu wani yawan maganganu daga PDP da zasu iya hana Buhari gyaran maidoma Najeriya mutuncinta ba a idan ya karkare.”
The post APC Maida Ma PDP Martani appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
No comments:
Post a Comment