Monday, 27 July 2015

PDP Ta Zargi Buhari Akan Tafiya Zuwa Amurka

Jam’iyyar PDP ta lissafa laifuffuka dayawa wadan suke zargin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta aikata. Sannan kuma Jam’iyyar tayi Allah wadai da furukin da shugaban Buhari yayi a Amurka.


Jaridar Punch ta lissafa  zaifufuka da yawa wadanda Jam’iyyar adawa ke zargin gwamnatin Shugaba Buhari. A cikin hadda rashin cin nasarar komai zuwan da yayi Amurka, da kuma wulakanta Patience Jonathan.


A ranar  Lahadi 26 ga watan, Olisa Metuh, maimagana PDP yace, daga Shugaba Buhari har Jam’iyyar shi APC babu wanda ya karu da wani abu a tafiyar. “Ziyarar tazo ta tafi, amma tsoron da mukeji shina babu wani abu da aka koya ko aka karu dashi a tafiyar. Babu abunda muka samu sai kace-nace, gardama, karyata zance da jin kunya. Hakan kuma ya faru ne saboda rashin wayewar kai da kuma sanin makamar aiki da shugabancin kasarnar nan da APC takeyi.  


“Miyakon ace sun samo wani taimako na musanman wajen yadda za a yaki yan ta’adda kamar yadda aka yi masu s lokacin Goodluck Jonathan, inda har sun kusa mika wuya, ba kamar yadda sukeyi a yanzu ba karkashin APC. A’a sai dai musanta zantuka wadanda sukayi da gwannatin Amurka data saukadda dashi. Wannan ba kawai kunyatar damu bane, wata manuniyace wannan gwamnatin  baza ta iya tafiyar da harkokin kasa da kasa ba.” Cewar Metuh.


Maimaganan yayi kira ga Shugaba Buhari da ya fuskanci yadda zai ya kawo karshen ta’addanci. Inda yayi tuni yadda shugaban yayi alkawari a hirar da  CNN tayi dashi a 2 ga watan Afrilla cewa zaya kawo karshen ta’addanci cikin wata biyu bayan rantsar dashi.


Metuh kuma ya ci gaba: “Yan Najeriya sun girgiza da zancen da Buhari yayi cewa, zaya tafiyadda Najeriya ta hanyar bin yadda launin zaben daya wuce ya nuna.”


Kungiyar din kuma yayi tuni da yadda Buhari ya fadama wasu yan Najeriya a Amurka cewa, a dukkanin gaskiyar magana, baza a Iya hada  mazabar data bada kashi 97 cikin Dari ba, da wadda ta bada kashi 5. Yace da alama gwamnatin na shirin nuna banbanci a cikin mulkinta.


“Ba a taba sanun wani shugaban kasa  da yayi irin wannan maganar nuna banbanci ba. Ba a taba samun wani shugaban kasa daya nuna shirin bibaya, da bangaranci da kuma raba kan kasar shi da mutanen shi ba kamar wanna. Shi na kowa ne, kuma ni ba na kowa bane” ya kawo kyakyawan tsammani mai kyau ga yan Najeriya. Amma furukin da yayi na nuna banbanci ya bata lamarin. Dole ya fito fili akan wanna magana. Shin wanna magana da yayi da ita zayayi amfani wajen nade-naden mulkinsa mai yakon yayi amfani da cancanta da hakkin kowane bangare (federal character) kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada? Shin da wannan ne za yayiamfani wajen nadin manyan Jami’an gwamnati, karin girman ma’aikata da shugabancin gwamnati?


“Shin da wannan ne za yayi amfani dashi wajen tallafama sashoshin kasarnan, aiyukan da gwamnati zata aiwatar miyakon gaskiya da kamanta adalci? Shin haka suma gwamnonin Jihohin APC zasuyi wajen nuna banbanci? Bari mu tuna ma shugaba Buhari cewa nuna banbanci ya saba ma rantsuwar kama aiki, Wanda kiri-kiri aka rubuta a cikin rantsuwar cewa ‘ Zaniyi aikin ba tare da nuna banbanci ba, San wani ko kin wani kalar yan kasa ba.”


Premium Times ta ruwaito cewa PDP kuma tayi Allah wadai da wulakanta wasu yan kasuwa ba da Buhari yayi a Amurka ba.  Metuh yace mun yadda Buhari Nada ikon da zaya sanya wadanda yaga dama cikin tawagar tafiyarshi ba. Amma yadda ya wulakanta yan kasuwan zaya isar da mugun sako ga yan kasuwa masu son zuba hannun jari a Najeriya.


“Wadannan yan kasuwan shugaban kasar su ya wulkanta su, amma Shugabannin wata kasa sun shigar da su taro a Amurka tare da Obama saboda hannun jarin da suke dashi a kasashen. Mun samun labari cewa rishin zauran yan kasuwan na Najeriya ya haifar da rishin zantawa mai kyau da zauran yan kasuwar na Amurka. Amma shi Obama yazo da cikakken taron mashawartanshi da yan kasuwa, shi kuma namu sai dai wasu gwamnoni na APC guda ukku masu halayen da za’a Iya zargin su, wadanda basu biyan albashi, hakan ya sanya ya hana Najeriya cin moriyan zantawar. Sai yasa ya na ce wajen tafiyar da Najeriya shi kadai ba tare da ya nada mukaman gwamnati masu amfani ba. Hakan za tilasta Jam’iyyar PDP ta bukaci gwamnatin shi ta wallafa kudaden data kashe Daga 29 ga watan Mayu zuwa yau. Mun bukaci hakan me saboda tun da aka nada gwamnatin APC bata nada mukamai masu mahimmanci ba. Hakan  yasa kudaden dake aljihun gwamnati suke ta ragewa. Hakan kuma yabada wani yanayin da za’a iyayin almundahana.”    


Metuh kuma yace: ”PDP na rike da wasu takardu dake nuna cewa Shugaba Buhari na tattaunawa da Bankin Duniya domin cin bashin dala biliyan 2.1 domin yayi wani abu Wanda babu wanda yasan komi Nene. Me nene bashi? Suwa ke aikin ciyo bashin? Minene yarjejeniyar cin bashin? Shin dagaske ne Buhari na kokarin cin bashin ne domin ya biya kudade da yawa da aka bashi taimako lokacin yakin neman zabe?”Metuh yake tambaya. Idan dai wannan gwamnatin nada gaskiya da bin tsari, ya kamata ta fito ta bayyana yadda ta kashe kudi cikin watanni biyu da hawan ta. Allah wadai da wulakancin da aka yima Patience Jonathan. Matar tsoron shugaban Kasannan an hana ta yin amfani da waje na musamman na filin Jirgin Kasa dake Fatakwal bayan an bada umurni Daga Abuja. Lokacin da Jonathan yake kan mulki, iyalan tsofaffin shugabannin kasa suna samun damar yin amfani da wajen na musamman.”



The post PDP Ta Zargi Buhari Akan Tafiya Zuwa Amurka appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.

No comments:

Post a Comment