Akwai wani dan Najeriya mai shekaru 30 da sunan, Nanso Odo ya rasa ransa bayan da ‘yan sanda sukayi mashi mugun bugu a Hilbrow a Johannesburg, Kudancin Afrika.
Rahotanni da Kamfanin dillacin labaru na Najeriya sun nuna cewa mamacin dan asalin Jihar Imo ne, ya rasu bayan da sukayi wata rigaya dan uwansa dan Najeriya a wajen sana’ar su a kudancin Afrika. Ikechuku Anyeye wanda shi ne shugaban kungiyar yan Najeriya masauna kudancin Afrika ya nuna matukar bakin cikin mutuwar Mista Odo.
Wannan abu ya matukar batama shugaban kungiyar Mista Anyeye rai, Inda yayi Allah wadai da aukuwar abun. Mista Emeka Ezinteje, Jami’i mai hudda da jama’a na kungiyar ya gayama kamfanin dillacin labafai a kasa (NAN) a Johannesburg, cewa mista Odo mai sana’ar aski ne, al’amarin ya faru be bayan sunyi fada da abokin sana’ar shi a wajen sana’ar. “Bayan sun gama fadan sai abokin sana’ar ya tsaida yan sanda masu zagaye, ganin hakan sai shi mista Odo ya ruga. Ganin hakan sai yan sanda suka bishi, bayan kimanin Minti 30 sai suka dawo da jikinshi babu rai. Saboda rishin gamusuwa, wasu yan kungiyar sun je har asibiti suka duba gawar” Cewar Ezinteje.
Wani rahoto kuma ya nuna cewa Sajent Nangabeni ya musanta cewa yan sanda ne suka kasheshi. Yace: “Mudai wani ne ya tari gaban mu Muka tsaya, shi kuma Mistake Odo ya ruga abinshi.”
Ezinteje Wanda rahotan shi yace kungiyar Na zargin akwai mummunan sa hannu a cikin. Kuma mun samu rahoto cewa mista Odo bugun shi akayi harya mutu. Amma mun sanya likitoci su duba mana sanadin mutuwar. Kuma wanna kungiyar zata kai maganar wajen sashen yan sanda masu bincike masu zaman kansu.
“Sashen shi keda alhakkin duba dukwani abu da yan sanda sukayi ba dai-dai ba.” Sannan yace sun sanar da karamin Ofishin Jakadancin Najeriya dake Johannesburg da kuma Ofisin yan sanda dake Hillbrow.
The post ‘Yan Sanda Kudancin Afrika Kashe Dan Najeriya appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
No comments:
Post a Comment