Pages

Thursday, 27 August 2015

Hukumar Zabe Ta Fiddo Da Wata Sabuwar Hanyar Hana Magudi

Hukumar zabe ta kasa (INEC) ta shirya yin amfani da wasu sabbin dabaru domin hana magudin zabe a zabukan Jihohin Kogi da Bayelsa da za’ayi.



Sabuwar dubarar zatayi amfani da yanar gizo ne wajen tattara sakamakon zabe na kowace mazaba.


Daraktan labarai da sadarwa na hukumar Chidi Nwafor ne ya bayyana hakan a jiya 26 ga watan Agusta a wani taro da Kungiyar Injiniyoyi ta kasa rashen Jihar Abuja ya hada mai suna ” Satin Injiniyanci da kuma taron duka manbobi “Engineering week and annual general meeting.”


Nwafor ya bayyana cewa wannan sabuwar hanya zatayi amfani ne da katin din din din domin tabbatar da zabe mai inganci.


Yace: “Mun sanya wata sabuwar hanya wadda zata idan sakamakon zabe ya taho daga mazaba sai a tura shi zuwa ward, wanda daga nan mataimakin ward zaya tura ma matattarar sakamakon zaben. Wannan hanya an gwada ta kuma anga tana yi lafiya lau. Sakamakon na zuwa zata ba kowane Jam’iyyar zabe nata kason.   


“Daga yanzu Yan Najeriya suyi tsammanin zabe mafi inganci a zaben da za’ayi a Kogi da Bayelsa. Samuwar wannan hanya da kuma Card reader zaya hana magudi.”


Note: There is a poll embedded within this post, please visit the site to participate in this post’s poll.



The post Hukumar Zabe Ta Fiddo Da Wata Sabuwar Hanyar Hana Magudi appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.

No comments:

Post a Comment