Jam’iyyar PDP ta roki mutanen Najeriya dasu shiga Jam’iyyar tasu. Mukaddashin Shugaban Jam’iyya, Uche Secondus ne ya bayyana haka a lokacin da ake rantsar da kwamitin yima yan Jam’iyya rajista ta yanar gizo.
Wannan na zuwa bayan da aka kada Jam’iyyar PDP daga kan mulki wata 5 da suka wuce bayan tayi sama da shekaru 16 tana mulki. Jam’iyyar ta bayyana cewa masu son shiga Jam’iyyar suna iya shiga. Kuma da sabo da tsohon dan Jam’iyyar duk za’a yi masu a dalci.
Mukaddashin Ciyaman din ya bayyana cewa neman yin rajistar ya zama dole a yanzu. Kuma uban gidanci ya kusa karewa a cikin Jam’iyar.
Secondus yace: “Zaku iya tunawa shawara rajista na yanar gizo ta dade. Muna kira ga duk yan Najeriya su zo su shiga wannan Jam’iyyar ta mu. Yan Jarida ma dake nan su zo su shiga su zama mambobin mu.”
Note: There is a poll embedded within this post, please visit the site to participate in this post’s poll.
The post Ku Shiga Jam’iyyar Mu – Cewar Shugabannin PDP appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
No comments:
Post a Comment