Friday 2 October 2015

Babu Sauran Uzuri Daga Wajen Buhari – Rabaren Okotie

Rabaren Fasto kuma dan Siyasa, Chris Okotie ya bayyana cewa babu sauran uzuri daga wajen Shugaba Muhammadu Buhari tunda ya aika da sunayen ministocin shi majalisar dattawa domin tantancewa.



Rabaran Fasto Chris Okotie

Rabaran Fasto Chris Okotie



Rabaren Okotie wanda shine Ciyaman Fresh Democratic Party (FDP), ya shawarci gwamnatin APC data canja akalar kudurorin ta a yanzu domin cigaban kasa.


A wani jawabi da aka fidda daga ofishin su dake Legas, yace:


“Kowace kasa na fuskantar matsaloli, amma abunda suke yi shine sai su kauda wadannan matsalolin. A Najeriya, mun kasa cigaba saboda shugabanci marar kyau.


“A yanzu ya kamata gwamnatin APC ta canza akalar muradun ta domin samu kudurorin cigaban kasa.”



The post Babu Sauran Uzuri Daga Wajen Buhari – Rabaren Okotie appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.

No comments:

Post a Comment