Friday 2 October 2015

Manyan Labarai Guda 10 Da Sukayi Fice A Ranar Alhamis

Naij.com ta tattara maku manyan labarai guda 10 wadanda sukayi fice a ranar Alhamis 1, ga watan Oktoba. Ku duba domin ku same su.



 


cake-independence

A lokacin murnar bikin yancin kai na 55 a Abuja a Alhamis 1, ga watan Oktoba



1. An Bayyana Sunayen Mutane 21 Da Buhari Ya Mika.


Bayan jiran da aka sha akan mutanen da Shugaba Muhammadu Buhari yake so yaba ministoci, sunayen sun bayyana yanzu ga baki dayan su.


2. Adams Oshiomhole Da Matar Shi Sun Tarbi Mataimakin Shugaban Kasa.


Hotunan matar Adams Oshiomhole, Clara ya sake watsuwa a kafafen sada zumunta bayan da suka tarbi bakuncin mataimakin shugaban kasa, Osinbajo, a Jihar.


3. Fayose Ya Kalubalanci Buhari.


Gwamnan Jihar Ekiti Ayodele Fayose ya kalubalanci Shugaba Muhammadu Buhari daya bayyana a’inafin dalilin daya sanya yake yin bincike. Sannan kuma ya sanya binciken ya isa har zuwa gwamnatocin baya.


4. Buhari, Osinbajo, Saraki Sun Halarci Bikin Yancin Kai.


An gudanar da bikin murnar yancin kai na 55 a fadar shugaban kasa inda Buhari, Osinbajo, Saraki da Dogara duka suka halarci taron.


5. Yadda Buhari Ya Sara Sunan Wani Tsohon Gwamna A Cikin Jerin Sunayen Ministoci.Yana gaba da mika sunayen ministocin nashi, Shugaba Buhari ya  sanya sunayen tsofaffin gwamnonin Legas, Ekiti, Anambara, da Rivers. Wadannan sune; Fashola, Fayemi, Nngegi, da Ameachi.


6. Buhari Ya Tabbatar Da Mika Sunayen Ministocin Shi.


Bayan jiran da aka sha wajen neman sanin sunayen Ministocin Buhari, shugaban kasan ya tabbatar a ranar 1 ga watan Oktoba cewa ya mika sunayen Ministocin nashi zuwa majalisar Dattawa domim tabbatar dasu.


7. Yan Boko Haram 80 Suka Mika Kansu.


A ranar 1 ga watan Oktoba, Kimanin Yan Boko Haram 80 ne suka mika kansu ga sojojin Najeriya.


8. Yan Boko Haram Sun Kashe Mutane A Lokacin Bikin Yancin Kai.


Wasu wadanda ake zargin yan Boko Haram ne sunyi shigar Mata inda suka kashe mutane da yawa a lokacin bikin murnar Yancin Kan Najeriya a Jihar Borno.


9. Ana Zargin Wani Kwashinan Yan Sanda Da Taimaka Ma Yan Boko Haram.


Jami’an Yan sanda na Jihar Jigawa sun zargi Kwamishinan yan Sanda na Jihar, Usman Tili da taimakawa yan Boko Haram a fakaice.


10 El Rufa’i Ya Sanya Dokar Ta Bace A Fannin Ilimi.


Inda yake magana a Filin wasanni na Ahmadu Bello a Kaduna, gwamnan ya bayyana sanya dokar ta baci a fannin ilimi a Jihar.



The post Manyan Labarai Guda 10 Da Sukayi Fice A Ranar Alhamis appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.

No comments:

Post a Comment