Friday 2 October 2015

Ku Goyi Bayan Gwamnatin Buhari – Amaechi

Tsohon Gwamnan Jihar Rivers, Chibuike Amaechi, ya roki yan Najeriya su goyi bayan gwamnatin Buhari domin a samu nasarar da ake son cinmawa.



Tsohon Gwamnan Jihar Rivers Rotimi Amaechi

Tsohon Gwamnan Jihar Rivers Rotimi Amaechi



Tsohon Gwamnan ya bayyana haka a ranar Alhamis 1, ga watan Oktoba a Fatakwal, birnin Jihar Rivers domin murnar ranar yancin kan Najeriya. Jaridar The Punch ta ruwaito.


Amaechi ya bayyana cewa kishin kasa da hadin kan Najeriya ne kawai sinadaran da ake bukata domin samun cigaban kasa. Ya bayyana cewa gwamnatin Buhari ta nuna niyar ta wajen kawo cigaba a Najeriya.







Yace: “Matsalar mu za’a iya kawo karshen ta idan aka samu hadin kai. Kishin kasa shine abunda muke bukata domin kada wahalar magaba ya tafi a banza.


   


“Wannan gwamnatin ta Buhari nada niyar kawo cigaba. Tana bukatar goyan bayan yan Najeriya domin a samu haka.”


   


Tsohon gwamnan kuma ya roki yan Najeriya a cigaba da adduo’i domin samaun zaman lafiya. Amaechi dai yana cikin wadanda ake tsamanin Shugaba Muhammadu Buhari ya tura sunayen su majalisar dattawa domin a tantance su a matsayin ministoci.


      




















The post Ku Goyi Bayan Gwamnatin Buhari – Amaechi appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.

No comments:

Post a Comment